Kungiyar 'Yan Majalissun Afirka Na Kan Matsayarta Na Kin Amincewa Da ICC
Shugaban kungiyar 'yan majalissun dokokin kasashen Afirka Roger Nkodo, ya jaddada matsayar kungiyar game da kin amincewa da matakin kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, don gane da batun kasar Sudan, da ma sauran matakai na rashin adalci wadanda a cewar sa kotun ke dauka kan nahiyar Afirka.
Mr. Nkodo wanda ke bayyana hakan a birnin Khartoum, ya ce, nahiyar Afirka ba ta bukatar hukunce- hukunce na wariya da kotun ta ICC ke gudanarwa.
Ya ce, kungiyar hadin kan Afirka tare da daukacin hukumomin ta, sun yi watsi da takardar neman damke shugaban kasar Sudan, duba da cewa hakan na kunshe da wata manufa ta siyasa, da nuna banbanci ga nahiyar ta Afirka.
A watan Maris na shekarar 2009 ne kotun ICC ta ba da sammacen damke shugaba Omar al-Bashir na Sudan, bisa zargin sa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur.