Magoya bayan Mugabet sun gudanar da zanga-zanga a kasar
Wata guda bayan zanga-zangar da 'yan adawa suka yi a kasar Zimbabwe, a yau magoya bayan Shugaba Mugabet sun gudanar da zanga-zangar goyon baya ga shugaban
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Harare ya habarta cewa Dubun dubatan magoya bayan Shugaban kasar Zimbabwe Robet Mugabet ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Shugaban a yau Laraba, magoya bayan sun yi amfani da manyan bas-bas gami da manyan motoci wajen tattaro magoya bayansu daga sauren jahohi gami kauyukan kasar , har ila yau mahalarta zanga-zangar na sanye da rigar dake dauke da photon shugaba Robet Mugabet mai shekaru 92 a Duniya.
A watan da ya gabata ne duban 'yan adawa suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da siyasar shugaban kasar kalkashin jagorancin Mourgan Tchageri a birnin Harare fadar shugaban kasar
A yayin da yake jawabi a gaban duban magoya bayan sa da suka halarci zanga-zanga Shugaban 'yan adawa mista Tchagarai ya tabbatar da cewa Shugaba Mugabet ba zai iya fitar da kasar ba daga cikin mawuyacin halin da take ciki domin haka wajibi ne shi da manbobin gwamnatinsa su dauki alhakin mawuyacin halin da suka jefa kasar.
Tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan milkin mallaka a shekarar 1980, Shugaba Mugabet ne ke jagorantar kasar.