Dubban Magoya Bayan Mogabe Sun Gudanar Da Gangamin Goyon Bayansa
Dubban magoya bayan shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe sun gudanar da gangamin nuna goyon bayansu gareshi a shirin da yake yi na fada da munafukai cikin jam'iyarsa ta ZANU-PF
Dubban magoya bayan shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe sun gudanar da gangamin nuna goyon bayansu gareshi a shirin da yake yi na fada da munafukai cikin jam'iyarsa ta ZANU-PF. Kamfanin dillancin labaran reuters ya kara da cewa a cikin gangamin wanda suka kira taron mutane miliyon guda a birnin Harere a jiya sun yi watsi da kiraye kirayen da ake ta watsawa na cewa shugaban ya kamu da cutar cancer kuma yakamata da sauka daga kan kujerar shugabancin kasar.
Majiyar jam'iyyar ta bayyana cewa a halin yanzu akwai bangarori biyu a cikin shuwagabannin jam'iyyar wadanda suke shirye shiryen maye gurbin shugaba mugabe ko bayan ya sauka ko kuma bayan mutuwarsa. Daga bangaren yana tare da mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa a yayin da dayan kuma yana tare da matar shugaban kasar Grace Mugabe.
Shugaba Mugabe dan shekara 92 shi ne shugaban kasar Zimbabew tun shekara 1980 a lokacinda kasar ta sami 'yencin kanta daga turawan Ingila yan mulkin mallaka.