Zanga -Zanga Ta Lashe Rayukan Mutane Biyu A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da masu adawa da shirin shugaban kasar Joseph Kabila na yin tazarce a kan karagar shugabancin kasar a karkashin gwamnatin rikon kwarya ya lashe rayukan mutane akalla biyu.
Dubban al'umma ne suka fito zanga-zangar lumana a sassa daban daban na kasar Dimokaradiyyar Congo a yau Alhamis domin bayyana rashin amincewarsu da hukuncin da kotun kula da kundin tsarin mulkin kasar ya zartar na amince da shirin shugaban kasar Joseph Kabila na ci gaba da zama a kan karagar shugabancin kasar a bayan karshen wa'adin mulkinsa a watan Disamban wannan shekara ta 2016 a karkashin gwamnatin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zabuka.
Yan sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar lumana a sassa daban daban na kasar ta hanyar amfani da iskar gas mai sanya hawaye lamarin da ya haifar da tarzoma har ya kai ga rasa ran mutum guda daga cikin masu zanga-zangar da na dan sanda daya sakamakon jifa da duwatsu baya ga jikkatan wasu fararen hula biyu a garin Goma fadar mulkin lardin Kivu ta Arewa a shiyar gabashin kasar.