Angola : Mutane 300 Sun Mutu Sanadin Zazzabin Shawara
Hukumar kiwan lafiya ta duniya, ta ce cutar shawara a Angola ta hadasa mutuwar sama da 300
Cutar data fara bula a birnin Luanda na kasar, an tabbatar da yaduwarta zuwa yankunan Afrika da dama da suka hada da tsakiya da yammacin Nahiyar.
Rahotan da Hukumar Lafiya ta MDD ta fitar wannan alhamis, ya rawaito cewa akalla mutane dubu 2,536 ne suka kamu da cutar inda 301 suka kwanta dama.
hukumomin kiwan lafiya a kasar ta Angola sun duk da gangami rigakafin da ake a inda cutar tafi kamari, yaduwar cutar bai ragu ba, face ta’azzara da yake.
WHO tayi gargadi cewa, cutar ta yadu har zuwa Congo inda mutane 41 suka kamu da ita, kana kuma an samu bullar ta a Kenya da China.
Duk da baiwa mutane sama da miliyan 7 rigakafin shawara a Angola, yaduwar ta bai ragu ba.
Marabin dai da a fuskanci bullar cutar kamar haka a Angola, tun dai bayan shekara 1986.
Babu dai wani magani tsayaye dake warka da mai dauke da shawara, cutar da sauro ke yaddata, da ta samo asali daga yankunan kurmin Afrika da latin Amurka, saidai a cewar masana sha'anin kiwan lafiya ana yin riga kafin cutar.