Karuwar Wadanda Su ka Mutu A Harin Ta'addancin Borno
Rahotanni daga Jahar Borno Sun ce; Adadin Wadanda Su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin kunar wake sun kai 58.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ambato cewa; Adadin mutanen da su ka mutu sanadin harin kunar bakin waken da aka kai wa 'yan gudun hijira, ya karu zuwa 58.
Tun da fari hukumar da ta ke kula da taimakon gaggawa ta Najeriya ( Nema) ta sanar da cewa; An kai harin kunar bakin wake akan sansanin 'yan gudun hijira a garin Dikwa mai nisan kilo mita 90 daga miaiduguri, na jahar Borno, ya ci rayukan mutane 35. Bugu da kari, wasu mutanen da adadinsu ya kai 78 sun jikkata
Harin wanda aka kai a lokacin da 'yan gudun hujirar su ke karbar abincin karya kumallo, da safiyar talata ya fara fitowa ne a jiya laraba.
Tare da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa an karya lagon kungiyar ta 'yan ta'adda, sai dai duk da haka a cikin kwanakiin bayan nan kungiyar tana kara kaimi wajen kai hare-haren kunar bakin waje.