Taron Koli Kan Harkar Tsaro A Najeriya
May 27, 2016 14:45 UTC
A Najeriya, A ranar 26 ga watan Mayu nan ce aka kammala taron koli na kasar kan harkar tsaro na shekara 2016.
Taron na kwanaki biyu daya gudana a Abuja, ya hada masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da kuma mahukunta da wakilan jama’a daga ciki gida da ketare.
Ambasada John Kambel na Amurka wanda ya halarci taron ya bukaci ganin an dakile ayyukan ta’adanci musamen na Boko Haram wadanda ke samun kudade ta hanyar fashi da makami.
ga dai rahoto wakilin mu na Abuja Muhammad Sani Abubakar
Tags