Sojojin Ruwan Italiya Sun Gano Gawawwakin Bakin Haure 45 A Tekun mediterranean
(last modified Sat, 28 May 2016 05:39:45 GMT )
May 28, 2016 05:39 UTC
  • Sojojin Ruwan Italiya Sun Gano Gawawwakin Bakin Haure 45 A Tekun mediterranean

Sojojin ruwan kasar Italiya da suke sanya ido a gabar tekun Mediterranea sun samu nasarar gano gawawwakin bakin haure 45 da suka nutse a tekun bayan da jirgin ruwan da ke dauke da su ya samu matsala.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada labarin cewa: Sojojin ruwan Italiya da suke sanya ido a gabar tekun Mediterranea sun kai dauki ga wani jirgin ruwa da yake dauke da bakin haure kimanin 130 a tekun Mediterranea a lokacin da jirgin ya samu matsala ya nutse da mutanen da suke cikinsa, inda suka ceto da dama daga cikin bakin haure, amma wasu sun bace, sai da a ci gaba da gudanar da bincike a tekun sun samu nasarar gano gawawwakin mutane akalla 45.

A ranar Larabar da ta gabata ma wani kwalekwale makare da bakin haure da aka kiyasta cewa sun kai kimanin 650 ya nutse da mutanen da suke cikinsa a taken na Mediterranea kusa da gabar tekun Libiya, inda aka samu hasarar rayuka masu yawa.