Sojojin Nigeria Sun Kubutarda Mutane 11,600 Daga Hannun Boko Haram
Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sojin kasar sun kubutar da yan Nigeria kimani 11,600 daga hannun kungiyar Boko Haram tun lokacinda ya hau kan kujerar shugabancin kasar shekara guda da ta gabata
Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana cewa soojin kasar sun kubutar da yan Nigeria kimani 11,600 daga hannun kungiyar Boko Haram tun lokacinda ya hau kan kujerar shugabancin kasar shekara guda da ta gabata. Shugaban ya bayyana haka ne a wani rahoto da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya rabawa yan jaridu a jiya jumma'a. Shugaban ya kara da cewa maida cibiyar sojojin Nigeia zuwa Birnin Maiduguri babban birnin Jihar Borno inda kungiyar boko Haram tafi barna ya taimaka sosao wajen cimma wannan nasara. Shugaban ya kuma kar da cewa a halin yanzu babu wani yanki na Nigeria dake karkashin ikon kungiyar Boko Haram a duk fadin kasar.
Shugaban ya zayyana wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekara guda da ta gabata , wadanda suka hada da tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, shari'a, Makamashi da wutan lantarki, da kuma tattalin arziki da kuma sauransu.
Rahoton ya kara da cewa gwamnatin kasar ta bada muhimmanci wajen ganin rundunar kasa da kasa ta yankin mai dakaru 8,500 tana ci gaba da aikinta kamar yadda ya dace. Har'ila yau ya zuwa yanzu rundunar ta karbi kudade dalar Amurka million 21 sannan zata sami wusu karin dala Miliyon 79 nan gaba don ciki dala miliyon 100 da ta yi alkawari tun farkon kama aiki.
Shugaban ya ce yaki da cin hanci da rashawa yana tafiya kamar yadda ya yakamata, don a halin yanzu akwai mutane da dama da suka gurafana a gaban kuliya kan lamarin. Ya kuma gudewa kasashen duniya musamman kasashen yamma kan gudumawar da suka bayar don dawo da kudaden kasar da aka sace.