Najeriya : An Sake Kaiwa Bututun Mai Hari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5932-najeriya_an_sake_kaiwa_bututun_mai_hari
A Najeriya an sake kaiwa wani bututun mai a yankin Neja Delta dake kudancin kasar hari, wanda ya kasance wani hari na uku a cikin mako guda a yankin mai arzikin man fatur a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 29, 2016 01:05 UTC
  • Najeriya : An Sake Kaiwa Bututun Mai Hari

A Najeriya an sake kaiwa wani bututun mai a yankin Neja Delta dake kudancin kasar hari, wanda ya kasance wani hari na uku a cikin mako guda a yankin mai arzikin man fatur a kasar.

Da jijibin safiyar Asabar din nan wani gungun tsageru na, dake kiran kan su (Niger Delta Avengers) sun kai hari wa bututun mai na (Creek Trunk Line ) mai tsawan kilomita 100 a jihar Neja.

kuma tuni tsagerun suka dauki alhakin kai harin a shafin su na twetter, tare da shan alwashin aikata wasu ayyukan makamanta wannan anan gaba.

ko baya ga bututan man, tsagerun na kai hari wa bututan iskar gas.

'yan NDA sun kai wasu hare-hare makamantan wannan kan kanfanonin mai na Amurka Chevron da kuma na kasar ta Najeriya NNPC.

Yau kusan watanni da dama da tsagerun Neja Delta (NDA) take kai hari ga bututan mai, lamarin daya hadasa hasara mai yawa ta gagan mai da ake fitarwa a yankin.

Alkaluma sun nuna cewa Najeriya data saba fitar da gagan mai miliyan 2,2 a rana, ta sinci kan da ganga miliyan 1,4 a yanzu, wanda ya kasance mafi karamci gare ta tun bayan shekara 1990.