An Kammala Taron Ministocin Cikin Gida Na UEMOA
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5935-an_kammala_taron_ministocin_cikin_gida_na_uemoa
A birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, an kammala taron Ministocin Cikin Gida na kungiyar tattalin da kudi ta kasashen yammacin Afirka, inda kasashen takwas mambobin kungiya suka cimma matsaya kan karfafa alaka tsakaninsu, ta bangaren yaki da ta'adanci.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 29, 2016 01:06 UTC
  • An Kammala Taron Ministocin Cikin Gida Na UEMOA

A birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, an kammala taron Ministocin Cikin Gida na kungiyar tattalin da kudi ta kasashen yammacin Afirka, inda kasashen takwas mambobin kungiya suka cimma matsaya kan karfafa alaka tsakaninsu, ta bangaren yaki da ta'adanci.

kasashen Burkina Faso, Mali da cote d'ivoire dai na daga cikin kasashen yankin da suka fuskanci hare-haren ta'adanci a baya bayan nan.

Daga cikin mataken da kasashen suka dauka hada samar da katin shaida dan kasa na zamani masu kunsheda cikakun bayanai (biometrique) tsakaninsu da kuma musayar bayanai domin shirin ko ta kwana dan dakile ayyukan ta'adancia shiyyar.

Baya ga ta'addanci, fataucin miyagun kwayoyi, makamai da jama'a, kaifin kishin addani, fashin teku, halatta kudade, da ma sauransu na kasancewa wani tushen babbar damuwa ga tsaron jama'a da dukiyoyinsu a shiyyar da ma zaman karko na kasashe mambobin kungiyar.

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall, shugaban kwamitin manyan jami'ai kan aiwatar da shirin zaman lafiya da tsaro, ya jaddada a nasa bangare bukatar yin aikin gaggawa gaban kalubalolin tsaro da kasashen shiyar suke fuskanta.

Haka kuma, ya jaddada wajabcin karfafa karfin sanya ido, nazari da yin rigakafi game da barazana a yankin na UEMOA.