Tsegerun Niger-Delta sun sake fasa bututan Mai
A karo na Uku cikin mako guda, Tsegerun Niger Delta Avengers dake kudancin Najeriya, sun sake kai hare-hare kan rijiyoyi da bututan man feturin kasar, lamarin dake sake nakasa tattalin arzikin kasar.
Hare-hare ‘yan tawayen Niger Delta kan bututan man a ‘yan watannin nan, ya rage adaddin gaggan mai da kasar ke fitarwa a ko wata rana daga gagga miliyan 2.2 zuwa miliyan 1.4.
A safiyarjiya Assabar ne ‘yan tawayen suka kai sabbin hare-hare kan bututan Man Nembe, kwana guda bayan daukan alhakin hari kan bututun Man gwamantin kasar na NNPC dake Warri, da kuma na kamfanin Chevron.
Kungiyar dai ta yi ikrarin kai hare-haren ne , tahanyar shafinta na Twitter, inda ta ce ta fasa bututai guda uku da suka hada tashar fitar da mai ta Brass da Bonny, a jihar Delta.
Kamfanonni Matatun Mai dake Kudanci Najeriya, Sun ce ci gaba da irin wannan hare-hare zai tilasta musu kwashe ma'aikatansu daga yankin.