Hukuncin Shekaru 20 A Kan Tsohuwar Matar Shugaban Ivory Coast
May 29, 2016 06:39 UTC
An yanke wa tsohuwar Matar Shugaban Iviry Coast hukunci shekaru 20 a gidan kaso
Kamfanin dillancin labaran Kasar Faransa ya habarta cewa babbar kotun kasar Cote D'ivoire ta tabbatar da hukuncin shekaru 20 a gidan Yari da aka yankewa Simoun Gbagbo tsohuwar matar shugaban kasar Cote D'ivoire Lauren Gbagbo saboda da lafin da aka kamata da shi na yin zagon kasa ga tsaron kasar.
Kotun ta yi watsi da bukatar Simoun Gbagbo na sake yin nazari kan hukuncin da aka yanke mata.
Baya ga wannan hukunci, a gobe ne ake sa ran za a sake gurfanar da Simon Gbagbo a gaban wata kotu dake birnin Abidjan kan wani sabon laifi na cin zarfin bil-adama a yayin yakin neman zabe na shekarun 2010-2011-da kuma 2012.
Tags