Shugaba Buhari Ya Bukaci 'Yan Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5959-shugaba_buhari_ya_bukaci_'yan_nijeriya_da_su_kara_hakuri_da_gwamnatinsa
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yabi 'yan kasar saboda irin hakuri da juriyar da suka nuna tsawon shekara guda na mulkinsa duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta yana mai kiransu da su kara hakuri da shirin gwamnatin nasa da gyara kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 29, 2016 10:37 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Bukaci 'Yan Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yabi 'yan kasar saboda irin hakuri da juriyar da suka nuna tsawon shekara guda na mulkinsa duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta yana mai kiransu da su kara hakuri da shirin gwamnatin nasa da gyara kasar.

Shugaba Buharin ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa al'ummar Nijeriya don tunawa da ranar demokradiyya kana kuma ranar da gwamnatinsa ta cika shekara guda inda ya ce tsawon shekara gudan gwamnatinsa ta samu nasarori a fannoni da dama, to amma duk da haka ya bukace 'yan Nijeriyan da su ci gaba da hakuri ganin irin mawuyacin halin da ya samu kasar a lokacin da ya karbi mulki daga hannun gwamnatin da ta gabata.

Shugaban ya ce tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyacin hali sakamakon faduwar farashin man fetur da kuma watandar da jami'an gwamnatin kasar da ta shude suka yi, to amma duk da haka yayi alkawari ci gaba da kokari wajen ganin an fita daga cikin wadannan matsalolin da suka addabi Nijeriyan.

Yayin da yake magana kan batun tsaro wanda ake ganin gwamnatin tasa ta samu gagarumar nasara, shugaba Buhari ya ce a halin yanzu babban aikin da ke gaban gwamnatin tasa shi ne batun sake tsugunar da mutanen da suka baro yankunansu sakamakon rikicin Boko Haram wanda ya ce ya zuwa yanzu an gama kassara su.

Yayin da yake magana kan tsagerun 'yan Niger Delta wadanda suke zaton kasa wa tattalin arzikin Nijeriyan, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta murkushe su duk kuwa da yace hakan ba zai hana su tattaunawa da shugabannin yankin Niger Delta din ba don magance matsalar da yankin ke fuskanta.