Gwamnatin Nigeria Zata Shiga Tattaunawa Da Shuwagabnnin Yankin Niger Deltar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5974-gwamnatin_nigeria_zata_shiga_tattaunawa_da_shuwagabnnin_yankin_niger_deltar
Shugaban mohammad Buhari na tarayyar Nigeria ya ce gwamnatinsa zata shiga tattaunawa da shuwagabannin yankin Niger Deltar
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 30, 2016 01:54 UTC
  • Gwamnatin Nigeria Zata Shiga Tattaunawa Da Shuwagabnnin Yankin Niger Deltar

Shugaban mohammad Buhari na tarayyar Nigeria ya ce gwamnatinsa zata shiga tattaunawa da shuwagabannin yankin Niger Deltar

Shugaban mohammad Buhari na tarayyar Nigeria ya ce gwamnatinsa zata shiga tattaunawa da shuwagabannin yankin Niger Deltar a dai dai lokacinda sojojinsa sunke ci gaba da fatattakar yan bindiga wadanda suke fasa bututan mai a yankin. Kamfanin dillacnin Labaran reuters shugaban yana fadar haka a jiya lahadi a wani jawabin da yayi don cika shekara guda a kan kujerar shugabancin kasar a jiya Lahadi. Barnan da matasan yankin Niger Deltar suke yiwa bututan man dai ya hana samuwar wutan lantarki a mafi yawan jihohin kasar, har 'ila yau ya rage yawan man fetur wanda kasar take sayarwa zuwa kasashen waje da kaso mai yawa. Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da share wuraren da aka gurbata da manfetur a yankin na Niger Deltar da kuma kyautata rayuwar mutanen yankin. A cikin yan kwanakin da suka gabata ne wata sabuwar kungiya wacce ta kira kanta da "Niger Delta Avengers militants" ta bullo a yankin take kuma daukar nauyin hare haren da ake kaiwa kan bututan man fetur a yankin. Har'ila yau kungiyar ta bukaci kamfanonin da suke hakar man fetur a yankin da su fice daga yankin cikin wata guda.