Wasu Tsoffin Mayakan Kungiyar Al-Shabab Sun Kashe Mutanen Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5977-wasu_tsoffin_mayakan_kungiyar_al_shabab_sun_kashe_mutanen_kenya
Tsoffin Mayakan al-shabab sun Kashe mutanen Kenya guda ukku a jiya Lahadi
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 30, 2016 01:54 UTC
  • Wasu Tsoffin Mayakan Kungiyar Al-Shabab Sun Kashe Mutanen Kenya

Tsoffin Mayakan al-shabab sun Kashe mutanen Kenya guda ukku a jiya Lahadi

Shugaban yansandan kasar Kenya ya bayyana cewa wasu tsoffin mayakan kungiyar Al-shabab ta kasar Somalia wadanda suka balle daga kungiyar sun kashe mutanen kasar da dama a jita Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Chunhuwa na kasar China ya nakalto Francis Wanjohi shugaban yan sandar kasar yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa mutane ukku ne tsoffin makayan kungiyar al-shabab suka kashe, amma har yanzun basu shiga hannun jami'an yansandan wadanda suke bin dudduginsu ba. Jami'in yan sandan ya kara da cewa mutanen kasar ta Kenya kimani 300 wadanda suke shiga kungiyar yan ta'adda ta Alshabab sun koma gida a cikin kwanan nan.