An yiwa 'yan kaso dubu biyu afuwa a Zimbabwe
May 30, 2016 05:43 UTC
A wani shiri na rake tsunkoson gidan yari, Kimanin mutane dubu biyu ne aka yiwa Afuwa a Kasar Zimbabwe
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto magabatan kasar Zimbabwe na cewa domin rake tsunkoson gidan yari, Gwamnati ta yiwa 'yan kaso dubu biyu Afuwa tare da sakin su daga gidan yari, daga cikin wadanda wannan Afuwa ta shafa a kwai Mata da kananen Yara 'yan kasa da shekaru 18.
Magabatan kasar sun ce wannan Afuwa ba ta shafi wadanda aka yiwa hukunci daurin rai da rai da kuma wadanda suka aikata babban laifi kamar fashi da makamai.
A baya dai 'yan gidan yarin tare da masu tsaransu sun koka kan matsalar karamcin abinci.
kimanin 'yan kaso dubu 20 ne a gidajen yarin na kasar Zimbabwe.
Tags