Shirin dakarun Najeriya na kawo karshen Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5995-shirin_dakarun_najeriya_na_kawo_karshen_boko_haram
Kakakin Sojin Najeriya ya sanar da wani sabon kudiri na kawar da Kungiyar Boko Haram
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 30, 2016 06:22 UTC
  • Shirin dakarun Najeriya na kawo karshen Boko Haram

Kakakin Sojin Najeriya ya sanar da wani sabon kudiri na kawar da Kungiyar Boko Haram

Cikin Wata Sanarwa da ya fitar yau Litinin, Kanar Sani Kuka Sheka ya yi alawadai da da harin Bom din da aka kai jiya a garin Biu, sannan kuma Yace Dakarun tsaron kasar za su iya kokarinsu domin dakile hare-haren ta'addanci da kuma kawo karshen kungiyar Boko Haram a kasar

A jiya Lahadi ne, Rundunar sojin Najeriya ta ce mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu uku na daban suka jikkata sakamakon fashewar wani abu da aka ce bam ne, a wajen garin Biu na jihar Borno mai fama da ayyukan Boko Haram.

Kakakin Rundunar Sojin Kanar Sani Usman ya ce Bam din ya tashi ne a kan titin Biu zuwa Damboa lokacin da wani babur mai kafa Uku ya take shi bisa kuskure.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wata mata da kuma jinjirinta.