Zanga-zangar masu fafutukar kafa daular Biafara A Najeriya
Kakakin 'yan sandar Niger-Dalta dake kudancin Najeriya ya bayyana damuwar sa kan yadda aka gudanar da zanga-zangar biafara
Akalla mutane bakwai aka tabbatar da mutuwarsu a arangamar da aka yi tsakanin jami’an 'yan sanda da masu fafutukar kafa kasar Biafra a Asaba da ke Jihar Delta.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Charlse Muka ya ce jami’an soja sun harbe biyar daga cikin masu fafutukar bayan sun kai hari kan ‘Yan Sanda suka kuma kashe biyu daga cikin su, tare da raunana wasu.
Rahotanni sun ce masu fafutukar sun kuma kai hari kan matafiya a hanyar Asaba zuwa Onitsha.
Amma ‘Yan sanda sun cafke wasu da dama daga cikinsu a Jihohin Enugu da Imo da ke yankin kudu masu gabashi.
A ranar Litinin ne dai masu fafutukar tabbatar da kafuwar Jamhuriyyar Biafran suka yi bikin cika shekara 50 da ayyana Jamhuriyyar ta Biafra.
Sai dai yayin da aka gudanar da bikin cikin lumana a wasu wuraren, a jihar Anambra an yi arangama tsakanin su da jami'an tsaro, inda ake zargin su da kashe wasu 'yan sanda da ma jama'ar gari.