Kenya: Zargin Kasashen Sudan Da Uganda Da Tsoma Baki A Harkokinta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6067-kenya_zargin_kasashen_sudan_da_uganda_da_tsoma_baki_a_harkokinta
Kakakin gwamnatin kasar Kenya ya ce; Sudan da Uganda suna son kifar da gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
Jun 01, 2016 03:28 UTC
  • Kenya: Zargin Kasashen Sudan Da Uganda Da Tsoma Baki A Harkokinta

Kakakin gwamnatin kasar Kenya ya ce; Sudan da Uganda suna son kifar da gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato kakakin gwamnatin kasar Kenya Eric Kiraithe ya zargi kasashen Uganda da Sudan da hada baki da wasu mutane a cikin Kenya din domin kifar da gwamnati.

Eric ya ci gaba da cewa; A cikin gida dole ne wadannan mutanen su kwana da sanin cewa; abinda su ke yi cin amanar kasa ne kuma za su iya gurfana a gaban shari'a.

Har ila yau, kakakin gwamnatin ya ce; Idan har bukata ta taso, to za a fallasa sunayensu ga 'yan kasa.

Furucin na kakakin gwamnatin Kenyar dai, ya zo ne a lokacin da 'yan adawar siyasa a cikin kasar su ka yi zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu akan shirye-shiryen zaben shugabankasa na gaba.

A shekara mai zuwa ta 2017 ne za a yi zaben shugaban kasar ta Kenya.