An Bukaci A Yiwa Hissen Habre Na Chadi Daurin Rai Da Rai
Feb 11, 2016 06:11 UTC
-
tsohon shugaban Chadi Hissene Habre a kotun birnin Dakar
Mbacke ya bukaci a yiwa Hissen Habre na Chadi daurin rai da rai
Babban alkalin kotun musamen ta Afrika dake yiwa tsohon shugaban kasar Chadi Hissen Habre shari'a ya bukaci da'a yi masa daurin rai-da-rai saboda zargin cin zarafin bil adama.
ko baya ga hakan al'aklin kotun mai suna Mbacke Fall ya bukaci a kwace ma tsohon shugaban kadarorinsa daya mallaka a matsayin wanda ya aikata muggan laifuka a lokacin mulkinsa a tsakanin shekarun (1982-1990)
Wani kwamitin bincike ya nuna cewa Hissen Habre nada zargin kashe mutane akalla 40,000 lokacin da ya jagoranci kasar.
Tags