Cote De Voire: mutuwar Sojojin Majalisar Dinkin Duniya 3
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6070-cote_de_voire_mutuwar_sojojin_majalisar_dinkin_duniya_3
Dakarun Tabbatar da zaman lafiya 3 na majalisar dinkin duniya ne su ka mutu a Cote De voire.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
Jun 01, 2016 03:28 UTC
  • Cote De Voire: mutuwar  Sojojin Majalisar Dinkin Duniya 3

Dakarun Tabbatar da zaman lafiya 3 na majalisar dinkin duniya ne su ka mutu a Cote De voire.

Kamfanin Dillancin Labaru na Xinhua ya ambato wata majiyar gwamnatin kasar ta Cote De Voire tana cewa; Sojoji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya ne su ka kwanta dama bayan hatsarin da motarsu ta yi.

Shugaban dakarun tabbatar da zaman lafiyar na majalisar dinkin duniyar a cote De Voire Aro Ladson, ya ce; sojojin da su ka mutu 'yan asalin kasar Senegal ne da ake shirin tura su zuwa kasar Afirka ta tsakiya.

Daga shekarar 2014 zuwa yanzu adadin dakarun majalisar dinkin duniya da su ka mutum a cikin kasar ta Cote De Voire sun kai 104.

Jim kadan bayan kawo karshen rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa ne a ka tura dakarun tabbatar da zaman lafiya kasar.