An Kame 'yan kungiyar al-shabab 4
Jun 01, 2016 07:59 UTC
Jami'an tsaron sun kame 'yan kungiyar al-shabab Kusa da Birnin Mogadishu.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinuha ya ambato kakakin ma'aikatar tsaron cikin gidan Somaliya Abdy Kumayl Mu'allim Shukry yana fadin cewa; An kame 'yan al-shabab din ne a cikin wata mota wcce su ka makare da bama-bamai.
Kumayl Shukri ya ci gaba da cewa; 'yan kungiyar ta al-shabab suna da shirin kai hari ne a cikin birnin Mogadishu.
A cikin watannin bayan nan dai sojojin kasar ta Somaliya tare da dakarun tabbatar da zaman lafiya na nahiyar Afirka sun tsananta kai hare-hare akan sansanonin 'yan kungiyar ta al-shabab, tare da samun galaba akansu.
Tags