Harin Kungiyar Boko Haram Ya Yi Sanadiyyar Kona Kananan Yara A Nigeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i61-harin_kungiyar_boko_haram_ya_yi_sanadiyyar_kona_kananan_yara_a_nigeriya
Harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar kan kauyen Dalori da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya a cikin dare ranar Asabar ya yi sanadiyyar kona kananan yara.
(last modified 2018-08-22T06:57:44+00:00 )
Feb 01, 2016 03:09 UTC
  • Harin Kungiyar Boko Haram Ya Yi Sanadiyyar Kona Kananan Yara A Nigeriya

Harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar kan kauyen Dalori da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya a cikin dare ranar Asabar ya yi sanadiyyar kona kananan yara.

Kamfanin dillancin Associated Press ya bada labarin cewa; Harin wuce gona da iri da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaddamar kan kauyen Dalori da ke gefen birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Nigeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa da ake kiyasta cewa sun doshi dari tare da jikkata wasu adadi masu yawa.

Shaidun ganin ido sun tabbatar da cewa harbi kan mai uwa da wabi da 'yan kungiyar Boko Haram suka din ga yi kan jama'a da gidajensu gami da cinna wuta kan gidajen, hakan ya yi sanadiyyar konewar mutane da dama musamman kananan yara jarirai da tsofaffi da marassa lafiya da masu da karfin tserewa.

Yan kungiyar ta Boko Haram sun shafe tsawon sa'o'i fiye da 4 suna cin karensu babu babbaka a kauyen na Dalori suna kwasar ganimar abinci da dabbobi, sannan suka kona kauyen.