An kai wani Mumunan hari a birnin Magadushu na Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6121-an_kai_wani_mumunan_hari_a_birnin_magadushu_na_somaliya
An kai wani kazamin hari cikin wani Otel dake karban bakuncin manyan mutane a birnin Mogadishu na kasar Somalia jim kadan bayan da kasar Amurka ta sanar da kashe jagoran Kungiyar AShabab Abdullahi Haji Da’ud a wani hari ta sama da Sojoji suka kai a cikin kasar
(last modified 2018-08-22T11:28:22+00:00 )
Jun 02, 2016 05:36 UTC
  • An kai wani Mumunan hari a birnin Magadushu na Somaliya

An kai wani kazamin hari cikin wani Otel dake karban bakuncin manyan mutane a birnin Mogadishu na kasar Somalia jim kadan bayan da kasar Amurka ta sanar da kashe jagoran Kungiyar AShabab Abdullahi Haji Da’ud a wani hari ta sama da Sojoji suka kai a cikin kasar

A jiya Laraba aka kai munanan hare-hare a wani kasaitaccen Otel mai suna Ambassador dake birnin Mogadishu inda manyan jami'ai na kasar da kuma baki ke zama.

Rahoton ya ce an ji karar fashewar bamai-bamai da kuma halbe-halben bindiga a harabar wannan Otel din, lamarin da ya sanya Majiyoyi da dama ke ganin cewa mutane da yawa ake ganin sun rasa rayukansu sakamakon wannan hari.

Wannan hari na ta'addanci na zuwa ne jim kadan bayan da Amurka ta sanar da hallaka Shugaban Kungiyar Ashabab din Abdullahi Haji Da’ud.

Peter Cook mai Magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya bayar a jiya Laraba.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikekken bayyani da ya fito daga bakin Gwamnatin kasar game da adadin mutanan da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata.

Duk da da cewa tun a shekarar 2011, Dakarun tabbatar da sulhu na kungiyar tarayyar Afirka suka fatattaki mayakan Ashabab din daga birnin Magadushu, amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a cikin kasar da kenya.