Murtaniya: An Kama 'yayan tsohon Shugaban Kasa
Jun 03, 2016 14:43 UTC
An Kame 'Ya'ya tsohon shugaban kasar Murtaniya biyu bisa zargin hada-hadar muggan kwayoyi.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato cewa a kasar ta Murtaniya an kame Sidy Muhammad da Ali Sheikh, da dukkaninsu 'ya'yan tsohon kasar ne Muhammad Khune, wanda ya yi mulki daga 1980 zuwa 1984.
Bugu da kari, an yanke wa mutanen biyu hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 15 da kuma 4 bisa laifin hada-hadar muggan kwayoyi.
Bugu da kari, kotun ta sami wasu mutanen biyu masu suna Ali Hamdy would Abubakar da al-maalum Would Ahamd Bilal da irin wadannan laifukan saboda haka aka daure su shekaru 11 da kuma goma.
Tags