Gunea Bissau: Sabon Pira minista ya yi rantsuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6205-gunea_bissau_sabon_pira_minista_ya_yi_rantsuwa
An rantsar da sabon Pira ministan kasar Gunea Bissau a yau juma'a.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 03, 2016 14:45 UTC
  • Gunea Bissau: Sabon Pira minista ya yi rantsuwa

An rantsar da sabon Pira ministan kasar Gunea Bissau a yau juma'a.

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) daga birnin Bissau ya nakalto cewa shugaban kasar Khoze Mario vaz ne ya ranstar da sabon pira ministan Baciro Dja.

Rantsar da sabon pira ministan dai ya zo ne, bayan wata dambaruwar siyasa a tsakanin 'yan majalisar zartarwa da kuma shugaban kasa. 'Yan majalisar zartarwar dai sun fara yajin aiki tun a ranar 15 ga watan Mayu, sai dai a jiya sun sake shiga ofis din nasu.

An sa ran cewa Dja zai zabi sabbin ministocin da zai yi aiki da su, sai dai ministocin na yanzu sun ce ba za su bar mukamansu ba.