An Soki Gajiyawar Majalisar Dinkin Duniya A Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6208-an_soki_gajiyawar_majalisar_dinkin_duniya_a_congo.
Kungiyoyin Farar Hula Sun yi Suka Akan Yadda Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Su ka ki Taimakawa 'Yan gudun hijirar Congo.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 03, 2016 14:47 UTC
  • An Soki Gajiyawar Majalisar Dinkin Duniya A Congo.

Kungiyoyin Farar Hula Sun yi Suka Akan Yadda Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Su ka ki Taimakawa 'Yan gudun hijirar Congo.

A yau juma'a ne kafar watsa labarun Africa Times ta ambaci cewa kungiyoyin fararen hula a kasar Demokradiyyar Congo su ka yi suka da kakkausar murya akan dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kasar su ke kin taimakawa 'yan gudun hijira a gabacin kasar.

Watanni biyu kenan a jere da kungiyoyin fararen hular na kasar Demokradiyyar Congo su ke yin suka akan rashin kyawun hanyar da ke zuwa yankin Mpati da ke gabacin kasar.

Rahoton ya ci gaba da cewa da akwai 'yan gudun hijira dubu 50 da su ke fuskantar rashin kyawun hanya a wannan yankin.

Har ila yau, kungiyoyin sun ce a lokacin da sojojin kasar ta D-Congo su ka kai farmaki akan 'yan tawayen kasa Rwanda, dakarun tabbatar da zaman lafiyar ba su taimakawa 'yan gudun hijirar ba, sannan kuma basu bada dama ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa ba da su isa yankin domin kai nasu daukin.

Matakin da kungiyoyin fararen hular su ke dauka ne ya sa wani jami'in tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a birnin Newyork ya yi furuci da cewa daya daga cikin matsalolin da 'yan gudun hijirar su ke fuskanta ita ce rashin kyawun hanyoyi.