Za'a Sokewa Zimbabuwe Bashi
-
Patrick Chinamasa, ministan kudi na kasar Zimbabuwe
Kasar Zimbabuwe ta sanar cewa ta samu alkawarin soke mata bashi daga abokan huldar ta, da suka hada da asusun bada lamuni na duniya, bankin duniya da kuma Bankin raya kasashen Afirka.
An cimma wannan alkawarin da zai fara aiki a watan Satumba mai zuwa, a wani taro hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, a daura da taron shekara-shekara na bankin raya kasashen Afrika daya gudana makon jiya a Lusaka.
A cewar ministan kudi na kasar ta Zimbabuwe Patrick Chinamasa, an dai gabatar da wannan bukata ce a watan Oktoba bara a birnin Lima na kasar Peru, sannan za'a gabatar da bukatar a taron shawara na Asusun IMF da bakin duniya a watan Satumba na wannan shekara.
kasar Zimbabuwe dai na famna da tarin bashi da yawan sa ya kai na $ Bilyan goma, kuma idan har soke bashin ya tabbata kasar zata samun damar lunfasawa domin farfado da tattalin arzikin ta daya fuskanci mumunan koma baya a 'yan shekarun nan.