An kashe 'Yan bokoharam Da Dama A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6256-an_kashe_'yan_bokoharam_da_dama_a_najeriya
Sojojin Najeriya Sun Kashe 'yan Bokoharam da dama a Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 05, 2016 03:01 UTC
  • An kashe 'Yan bokoharam Da Dama A Najeriya

Sojojin Najeriya Sun Kashe 'yan Bokoharam da dama a Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato majiyar sojojin kasar ta Najeriya na sanarwa a jiya asabar cewa; Sun kashe 'yan kungiyar bokoaram 19 a jahar Borno.

Sanarwar Sojan ta ci gaba da cewa sun sami bayanai ne akan inda 'yan kungiyar a bokoharam a wani sansani.

Daga cikin wadanda aka kashe a lokacin wannan harin kamar yadda majiyar sojoin kasar ta ce; Da kawai Amir Abubakar Gana daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta Bokoharam.

Wata majiyar ta ce sojoji biyu ne su ka jikkata sanadiyyar harin.

Daga bullar bokoharam a Najeriya a 2009 zuwa yanzu, sun kashe fiye da mutane 10,000, yayin da wasu dubun dubata su ka zama 'yan gudun hijira.