Kwalara ta ci rayukan mutane da dama a kasar Congo.
A wasu sassa na arewacin kasar Congo mutane da dama sun rasa rayukansu sanadin bullar kwalara.
Ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ta kasar Congo ta yi gargadin cewa idan har ba a rika kula da batutuwa na kiwon lafiya ba, musamman ma dai a akan ruwa, to cutar za ta iya yaduwa a yankin arewain kasar.
Kawo ya zuwa yanzu dai an tabbatar da kamuwar mutane 368 da cutar a yankin Equadro da ke arawacin kasar.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato cewa; tuni mahukunta a kasar su ka zage damtse wajen magance matsalar ta hanyar wayar da kan mutane akan tsafta da kuma yi wa wadanda su ka kamu allurai.
Tuni ita ma hukumar lafiya ta duniya w.h.o ta yi alkawalin shiga cikin lamarin domin taimakawa.