Bunkasa Harkokin Tsaro A Somaliya:
Dakarun Tabbatar da zaman lafiya na Afirka da suke a Somaliya na bunkasa zaman lafiya.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar dakarun tabbatar da zaman lafiyar na nahiyar Afirka su na cewa za su kara tabbatar da tsaro a yayin zaben da za a yi a kasar a cikin watan Augusta na wannan shekara.
Wakilin kungiyar tarayyar Afirka a kasar ta Somaliya Francisco Madeira ya fada a wani bayanin da ya fitar a jiya asabar cewa; Zaben da za a yi a wannan shekara ta 2016 wani karin ci gaba ne da zai share fagen zaben da za a yi a 2020.
Madeira ya kuma ce; Dakarun na tabbatar da zaman lafiya da kuma hadin guiwar sojojin gwamnarin kasar ta Somaliya suna aiki tare domin tattauna yadda za a sanya idanu akan zaben da za a yi ta fuskar tsaro.
Somaliya dai tana fama da matsalar kungiyar al-shabab.