An Kame Wasu 'Yan Kasashen Waje Na Masu hakar Zinariya A Mauritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6280-an_kame_wasu_'yan_kasashen_waje_na_masu_hakar_zinariya_a_mauritaniya
Majiyoyin tsaro a Mauritaniya sun sanar da kame wasu mutane 'yan kasashen waje da suke gudanar da ayyukan hakar zinariya akasar ba bisa ka'ida ba.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 05, 2016 06:45 UTC
  • An Kame Wasu 'Yan Kasashen Waje Na Masu hakar Zinariya A Mauritaniya

Majiyoyin tsaro a Mauritaniya sun sanar da kame wasu mutane 'yan kasashen waje da suke gudanar da ayyukan hakar zinariya akasar ba bisa ka'ida ba.

Shafin labarai na Afrika Time ne ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron Mauritaniya sun kame mutanen ne su 11 da suka fito daga kasashen Chadi da Sudan, suna gudanar da aikin hakar zinariya a yankin Tamchekett da ke kudancin mauritaniya.

Bayanin ya ce mutanen baya ga cewa dukakninsu sun shigo cikin kasar ne ta hanyar kasar Mali ba bisa kaida ba, sun kuma shiga gudanar da wani aiki wanda shi ma ba bisa kaida suke yinsa ba, yanzu haka dai ana tsare da su kuma ana gudanar da bicike kan lamarinsu.