An fara tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6298-an_fara_tattaunawa_tsakanin_sudan_da_sudan_ta_kudu
A kokarin dinke barakar dake tsakanin kasashen biyu, magabatan birnin Juba sun ziyarci birnin Khartum domin ci gaba da tattaunawa
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 06, 2016 01:04 UTC
  • An fara tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

A kokarin dinke barakar dake tsakanin kasashen biyu, magabatan birnin Juba sun ziyarci birnin Khartum domin ci gaba da tattaunawa

Tun bayan girka gwamnatin hadin kan 'yan kasa a Sudan ta Kudu wannan shi ne karo na farko da ake irin wannan tattauna wa a birnin Khartum tsakanin bangarorin.

Tawagar dai ta Sudan ta Kudu ta kumshi ministocin harkokin waje, da na tsaro, da ministan cikin gida da na man fetir, inda suke gana wa da takwarorinsu na Sudan a birnin Khartum, a wani mataki na neman warware dumbun matsalolin da ke tsakanin su, da suka shafi batun 'yantar da kasar ta Sudan ta Kudu wanda ya wakana a shekara ta 2011.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen kasar ta Sudan ta Kudu Deng Alor, ya ce ya iso da wani sako na Shugaba Salva Kiir ga Shugaba Omar al Bashir na Sudan, wanda ya yi kira da a gaggauta magance matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu.

Kasashen Sudan da Sudan ta kudu na da sababi mai yawa a tsakanin su, daga cikin ana iya ambato batun yankin Aby da kasashen biyu suke jayayya kansa da kuma batun fitar da danyan man a kasuwanin Duniya wanda dole ne kasar Sudan ta kudun sai ta yi amfani da kasar Sudan kafin ta fitar da shi.

A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan din, amma bayan shekaru biyu kacal kasar ta fada cikin yakin basasa bayan da Shugaba Salva Kiir ya kori mataimakin Riek Machar.

A cikin shekaru biyu na yakin dubun 'yan kasar ne suka rasa rayukansu a yayin da wsu kimanin million biyu suka yi hijira