An kame wasu Sojojin Dakarun Sulhu na Afirka a Somaliya
An cabke wasu daga cikin Dakarun sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka kan zarkin su da sace man fetur gami da kayan aikin soja a Somaliya
Mohamed Hassan Hamoud jami'in 'yan sandar Somaliya ya sanar da cewa kimanin mutane 15 ne aka kame daga cikin su a kwai Sojojin Dakarun kasashen Afirka wato Amison 5 kan zarkin su da satar Man fetur gami da kayan aikin Soja .
Rahoton ya ce an kame fararen hula 10 ne a kasuwar bayan fage suna sayar da man fetur kayan aikin soja da sauransu a jiya Lahadi, bayan gudanar da bincike aka gano cewa wasu daga cikin Dakarun kungiyar Sulhu na Kasashen Afirka ne ke sato kayan ,su kuma wadannan Mutane su sayar da su a kasuwar bayan fage.
A nasa bangare Ministan tsaron kasar Somaliya Abdirisak Omar Mohamed ya ce da zarar an kamala bincike za a gurfanar da wadanda ake zarki a gaban kuliya.
Wannan dai shi ne karo na farko da magabatan Somaliyan ke tsare da wasu Sojoji daga cikin Dakarun sulhu na kasashen Afirka.
Dakarun sulhu na kasashen Afirkan wato Amison sun je kasar Somaliyan ne domin yaki da ta'addanci na kungiyar Ashabab.