Buhari Zai Je Landon Don Neman Magani
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6319-buhari_zai_je_landon_don_neman_magani
Shugaban Najeriya Muhammadu zai fara wani hutu na kwanaki goma daga wannan Litinin don kula da lafiyarsa.
(last modified 2018-08-22T06:58:24+00:00 )
Jun 06, 2016 06:15 UTC
  • Buhari Zai Je Landon Don Neman Magani

Shugaban Najeriya Muhammadu zai fara wani hutu na kwanaki goma daga wannan Litinin don kula da lafiyarsa.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai ta ce, Buhari zai tafi Landon domin neman magani a tsawan wannan lokacin.

Femi Adeshina ya ce tafiyar ta biyo bayan shawarwarin da likitoci suka bawa shugaban kasar don samun kula na musamman daga kwararru saboda ciwon kunnen dake damunsa.