Fadar Shugaban Nigeria Ta Bukaci Addu'a Ga Shugaba Buhari
Fadar shugaban Nijeriya ta bukaci illahirin al'ummar kasar da su sanya shugaba Muhammadu Buhari cikin addu'a a daidai lokacin da ya ke fara wani hutu na kwanaki 10 don tafiya birnin London don neman maganin ciwon kunnen da ya ke fama da shi da ya hana shi gudanar da wasu ayyukan da aka tsara zai gudanar.
Mai ba wa shugaba Buharin shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ne yayi wannan kiran a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau din nan jim kadan kafin shugaban ya tashi zuwa birnin na London a yau din nan don ganawa da likitocinsa inda ya ce yana kiran 'yan Nijeriyan da su yi wa shugaban fatan alheri da kuma samun sauki a yayin wannan ziyara tasa ta neman magani, yana mai cewa lafiya da mutuwa suna hannun Allah ne amma dai babu wani damuwa ainun dangane da halin da shugaban yake ciki.
Mr. Adeshina wanda shi ne ya fitar da sanarwar cewa shugaba Buharin zai tafi London wajen neman maganin ciwon kunnen da yake fama da shi yayi watsi da maganganun da wasu suke ta yadawa na cewa shugaban yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya; yana mai cewa har zuwa lokacin da shugaban ya tashi zuwa London din yana gudanar da ayyukan na office don haka babu wata magana ta cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.
A safiyar yau ne dai shugaba Muhammadu Buharin ya bar Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya don tafiya London bisa shawarwarin likitocinsa na cikin gida don ganawa da likitocinsa kan ciwon kunnen da ya ke fama da shi wanda ake ganin shi ne ya hana shi gudanar da wasu ayyuka na fili da suka hada da ziyarar da aka shirya zai kai Lagos da kuma yankin Niger Delta a kwanakin baya.