Jaddada Sunan Sudan cikin Jerin Kasashe masu Tallafawa Ta'addanci
Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana damuwarta da ci gaba da sanya kasar cikin jerin kasashe masu tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya na ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka.
Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana damuwarta da ci gaba da sanya kasar cikin jerin kasashe masu tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya na ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan tana bayyana haka a jiya Litinin ta kuma kara da cewa tare da duk hadin kai wanda gwamnatin kasar Sudan ta bayar bata ji dadin cewa har hanzu a kwai sunanta a cikin jerin sunayen cikin kasashen masu tallafawa ayyukan ta'addanci a kundin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ba. Ma'aikatar da musanta dukkan tuhume tuumen da wasu hukumomi a kasar Amurka takewa gwamnatin kasar kan abinda ya shafi ayyukan ta'addanci a duniya.
Tun shekara ta 1993 gwamnatin kasar Amurka ta sanya Sudan a cikin jerin kasashe masu tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya, sannan ta fara doramata dakunkumai a kan wannan lamari a shekara ta 1997.