Mai Yuwa Jinyar Shugaba Mohammadu Buhari A London Ya Wuce Kwanaki 10
Mai yuwa Shugaba Mohammadu Buhari Ya wuce kwanaki 10 A Jinyan da yake yi a birnin London, don yana fama da mura mai tsanani
Shafin yada labarai ta Sahara reporter ya gano cewa mai yuwa jinyan da shugaba Muhammadu Buhari yake yi a birnin Londan ya dara kwanaki 10 da aka bayyana, don kafin cutar kunne shugaban yana fama da tsananin mura wanda shima ya dade yana damunsa. Mr Femi Adesina babban mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai ne ya bayyana haka a jiya Litinin. A makon da ya gabata ne shugaban ya dage tafiye tafiyen da ya shirya zuwa Lagos, Ogoni da kuma Senegal don halattan taron ECOWAS saboda dalilan rashin lafiyarsa. A jiya litinin ne shugaban ya isa Londan tare da tawagarsa ta mutane 10 wadanda suka hada da likitansa Dr. Sanusi Rafindadi, Lawal Kazaure da kuma da wasu jami'an tsaronsa da Kukunsa.
Ana saran shugaban zai zauna a Abuja house na ofishin jakadancin Nigeria a birnin Londan sanna mai yuwa a yi mai aiki a kunnen nasa idan bukatar haka ta kama.