Gwamnatin Najeriya Ta Kirayi 'Yan Bindiga Na Niger Delta Avengers Zuwa Tattaunawa
Gwamnatin Najeriya ta kirayi 'yan bindiga na Niger Delta Avengers zuwa ga tattaunawa, domin samun sulhu da fahimta juna.
Kamfanin dillanicn labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Emmanuel Ibe Kachikwu babban jami'in gwamnati mai sanya ido a kan harkokin hakar mai a yankin ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya umarci dakarun kasar ad su daina kai hare-hare a yankin na tsawon makonni biyu, domin samun damar tattaunawa da 'yan bindigar.
Ya ce yanzu haka suna cikin kokarin ganin an samu daidaiton baki a tsakanin shugabannin kabilun yankin, domin zama kan teburin tatatunawa a tsakaninsu da matasan, wanda kuma hakan zai bayar da damar zama tare da da bangaren gwamnati, domin warware matsaloli da kuma korafe-korafen da suke da su domin shawo aknsu.
Hare-haren na Niger Delta Avengers dai ya kawo babban koma baya ga harkar hakar mai da kuma fitar da shi daga Najeriya, inda yanzu Najeriya ba ta iya fitar da ko da ganga miliyan daya, inda a lokutan baya take fitar da ganga miliyan biyu da rabi.