Najeriya : Tsagerun Niger-delta Sun Yi Fatali Da Bukatar Tattaunawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6430-najeriya_tsagerun_niger_delta_sun_yi_fatali_da_bukatar_tattaunawa
'Yan a ware na Niger-delta Avangers sun yi fatali da bukatar gwamnatin Nigeria ta tattaunawa.
(last modified 2018-08-22T06:58:24+00:00 )
Jun 08, 2016 06:47 UTC
  • Najeriya : Tsagerun Niger-delta Sun Yi Fatali Da Bukatar Tattaunawa

'Yan a ware na Niger-delta Avangers sun yi fatali da bukatar gwamnatin Nigeria ta tattaunawa.

A cikin wata sanarwa da tsagerun na NDA suka wallafa a shafinsu na Twitter, sun ce babu batun wata tattaunawa da duk wani kwamiti.

 

A ranar Litinin nan ce dai babban sakataren gwamnatin Nigeria na man fetur, Emmanuel Ibe Kachikwu ya sanar ga manema labarai cewa an dakatar da duk wani yunkuri soji a yankin na Niger- delta na akalla tsawan mako biyu domin baiwa kowa da kowa damar shiga tattaunawa.

 

Hare-haren da 'yan Niger delta ke kaiwa kan bututan man fetur sun dai harfar da kasar mumunan koma baya harkokin fitar da man fetur din da ta dogara dashi.