Najeriya : Stephen Keshi Ya Rasu
Jun 08, 2016 06:52 UTC
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta sanar da mutuwar tsohon Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar wanda kuma shi ne tsohon kocin Super Eagles, Stephen Keshi.
Mista Keshi ya rasu ne da tsakar daren ranar Talata a birnin Benin da jihar Edo yana da shekaru 54.
Emmanuel Ado dake Magana da yawun iyalan sa yace Keshi ya gamu da bugun zuciya a daren jiya a dai dai lokacin da yake shirin barin Najeriya.
Harwayau Mr Keshi shi ne dan Afirka na biyu da ya lashe kofin nahiyar Afirka a matsayin dan kwallo da kuma mai horar da ‘yan wasa, bayan Mahmoud El-Ghohary.
Kazalika Mr Keshi Ya jagoranci Togo da Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya, kana kuma ya horar da kasar Mali.
Tags