Gwamnatin Sudan ta yi watsi da bukatar 'yan tawayen yankin Darfur
Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa ba zata amince da duk wata bukata da ta sabawa yarjejjeniyar sulhun da aka cimma a birnin Dauha na Kasar Qatar
Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China daga Birnin Khartoum ya nakalto Amir Hasan Umar Shugaban tawagar Gwamnatin Sudan a tattaunawar sulhu da 'yan tawayen yankin Darfur na birnin Dauha a yau Laraba na cewa Gwamnati ba ta za ta amince da wata sabuwar bukata daga bangaren 'yan tawayen ba, saboda yarjejjeniyar sulhun da aka cimma wa tsanakin bangarorin biyu a birnin Dauha ya zamanto wani bangare na kundin tsarin milkin kasar don haka babu abinda zai sanya a dawo baya dangane da wannan batu.
Hasan Umar ya tabbatar da cewa duk wata tattaunawa da za a yi tare da bangaren 'yan tawayen za ta kasance ci gaba ga yarjejjeniyar birni Dauha ne.
A bangare guda, Shugaban kungiyar 'yan tawaye masu fafutukar 'yantar da yankin Darfur da ake kira da DDPD ya ce ba za su amince da yarjejjeniyar da aka cimma wa a baya ta birnin Dauha, idan kuma Gwamnati ta dage a kan wannan yarjejjeniya, to babu shakka za su bar tebirin tattaunawar.
A yayin da ake gudanar da wata sabuwar tattaunawa tsakanin Gwamnati Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen Darfur bisa shiga tsakanin magabatan kasar Qatar a birnin Dauha , ya zuwa yanzu tattaunawar ta kasa samun amincewar dukkanin kungiyoyin 'yan tawayen, lamarin da ya sanya aka kasa cimma matsaya guda.