Tsagerun Niger-Delta na ci gaba da barna a Najeriya
A yayi da ta yi watsi da tayin neman sulhu da gwamnatin kasar ta yi mata a farkon wannan mako kungiyar 'yan tawayen Niger Delta Avengers ta sake tarwatsa wata rijiyar man fetur a yankin.
Kungiyar ta sanar da wannan matsayi nata ne a cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a wanann Laraba, inda ta ce babu wata tattaunawa da ta soma da wani kwamiti, kuma idan har gwamnatin Najeriyar ta ce ta soma tattaunawa da wasu Kungiyoyin 'yan tawayen na yankin na Niger Delta, to Kungiyoyin na wakiltar kansu ne kadai.
Baya ga hakan kungiyar ta sanar da tarwatsa wata rijiyar man fetur din kasar dake yankin.
A ranar Litanin din da ta gabata ce sakataran kasa mai kula da harakokin man fetur na Najeriyar Emmanuel Ibe Kachikwu ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin Najeriya za ta dakatar da matakan soja da ta dauka a yankin na Niger Delta a baya bayan nan, har na tsawon mako daya zuwa biyu domin hawa tebirin tattaunawa da kungiyoyin 'yan tawayen yankin.
Harin da tsagerun Niger Delta na Avengers ke kaiwa kan rijiyoyin da bututun man fetur a yankin yayi babbar illa ga tattalin arzikin kasar,inda yayi sanadiyar raguwar danyan Man fetur din da kasar ke sayarwa a kasuwanin duniya da sama da kashi 50%.