Wani Biri ya yi sanadiyar daukewar wutar Lantarki a kasar Kenya
Jun 08, 2016 13:25 UTC
Biri ya janyo katsewar wutar lantarki a kasar kenya baki daya.
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya habarta cewa a yau Laraba Wani biri ya janyo daukewar wuta a kasar Kenya baki daya bayan ya fada kan wata na'ura mai muhimmanci wajen samar da wutar lantarki ga kasar.
Kamfanin samar da wutar lantarki, KenGen ya ce birin ya fada kan wata transfoma ne a tashar samar da wuta ta Gitaru da ke tsakiyar Kenyar.
Bayan birin ya fada kan tranfomar sai wuta ta dauke dalilin da yasa kasar ta yi asarar ma'aunin wutar lantarki megawatts 180 wanda hakan kuma yasa aka dauke wuta a kasar baki daya.
KenGen ya kuma ce an dawo da wutar bayan tsawon sa'oi hudu kuma birin bai mutu.
Tags