Somaliya Za Ta Karbi 'Yan gudun hijirar Dadaab na kasar Kenya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6466-somaliya_za_ta_karbi_'yan_gudun_hijirar_dadaab_na_kasar_kenya.
Shugaban kasar Somaliya ya ce; Za su karbi Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab idan Kenya ta rufe.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 02:13 UTC
  • Somaliya Za Ta Karbi 'Yan gudun hijirar Dadaab na kasar Kenya.

Shugaban kasar Somaliya ya ce; Za su karbi Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab idan Kenya ta rufe.

Kamfanin DIllancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato shugaban Somaliya Hasan Sheikh Mahmud wanda ya ziyarci kasar Kenya yana cewa; Somaliya tana da karfin da za ta daukar nauyin 'yan gudun hijira 300,000, wadanda dama 'yan kasar ne da suka nemi mafaka a kasar.

Shugaban na Somaliya wanda ya gabatar da tsaron manema labaru da takwaransa na Kenya uhuru Kanyatta ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kawo daukin jigilar 'yan gudun hijirar zuwa kasarsa.

Sansanin 'yan gudun hijirar Dadadb shi ne mafi girma a duniya a kasar Kenya. Sai dai kasar Kenya ta yi alkawalin rufe shi nan da wani lokaci.

Daga cikin dalilan da kasar ta Kenya ta bijiro da su domin rue, sansanin da akwai matsalar tsaro da su ke fuskanta daga kungiyar al-shabab.