Al'Shabab Ta Kashe Sojojin Habasha 40 A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6478-al'shabab_ta_kashe_sojojin_habasha_40_a_somaliya
Kungiyar Al'shabab ta sanar da kai wani hari kan sojojin tabbatar da zamen lafiya na Amisom dake Somaliya,
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 06:47 UTC
  • Al'Shabab Ta Kashe Sojojin Habasha 40 A Somaliya

Kungiyar Al'shabab ta sanar da kai wani hari kan sojojin tabbatar da zamen lafiya na Amisom dake Somaliya,

A sanarwar data fitar a shafin ta na Telegram kungiyar ta ce ta kashe sojojin Habasha sama da 40 a harin data kai a sansanin sojojin dake yankin Halgan a jihar Hiran.

 

Wasu ganau sun ce mayakan na Al'shabab sun kai harin ne bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kan sa a cikin wata mota a harabar sansanin, kafin daga bisani sauran mayakan sun farmawa sansanin tare da bude wuta kan jama'a.

 

Wannan dai ba shi ne karon farko da mayakan na Al'shabab ke amfani da irin wannan salo wajen kai hariwa dakarun sulhu na tarraya Afirka, inda ko a watan janairun daya gabata, wani hari makamacin wannan yayi sanadin mutuwar sojojin Kenya sama da 100.