An Kawo Karshen Ebola A Laberia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6487-an_kawo_karshen_ebola_a_laberia
Ma'aikatar lafiya a Laberia ta sanar da kawo karshen yaduwar annobar Ebola a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 06:48 UTC
  • An Kawo Karshen Ebola A Laberia

Ma'aikatar lafiya a Laberia ta sanar da kawo karshen yaduwar annobar Ebola a kasar.

Laberia ta kasance kasa ta karshe inda cutar ta gagara tun dai bayan bullar ta a yammacin Afirka.

kasancewa kasar ta shafe kwanaki 42 ba tare da samun sabon kamuwa da cutar ba, hakan na nifin an sake dakile yaduwar cutar a cewar ministan lafiya na kasar.

Bisa ga sharidan hukumar lafiya ta duniya ana ayyana kawo karshen cutar Ebola a wata kasa idan har aka kwashe kwanaki 21 ba tare da samun sabon kamuwa da cutar ba.