Gwamnatin Tarayyar Nigeria Zata Fara Aikin Tantance Malaman Makarantu 500,000
Gwamnatinn tarayyar Nigeria zata fara shirin tantance malaman makarantu 500,000 a ranar 12 ga watan Yunin da muke ciki.
Gwamnatinn tarayyar Nigeria zata fara shirin tantance malaman makarantu 500,000 a ranar 12 ga watan Yunin da muke ciki. Jaridar Daily Trust ta nakalto babban mai bawa mataimakin shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mr Laolu Akande yana fadar haka a yau ya kuma kara da cewa za'a bude shafin yanar gizo mai adrishe npower.gov.ng a ranar 11 ga watan yuni da muke ciki. Dan haka akwai bukatar matasa wadanda suka kammala karatu sun gabatar da kawukansu don wannan aikin wanda zai dauki shekaru biyu cutar ana gudanarwa.
Akande ya kara da cewa banda albashin naira dubu 23,000 da zasu karba ko wani wata za'a basu Komfuta wanda zai taimaka masu wajen horaswa da kuma ci gaba da taimakama masu wajen ayyuukansu.