Benin : An Dage Zaben Shugaban Kasa Zagayen Farko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i652-benin_an_dage_zaben_shugaban_kasa_zagayen_farko
An dai dage zaben ne saboda kasa raba daukacin katinan zabe
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 12, 2016 05:13 UTC
  • Shugaba Boni Yayi na Benin
    Shugaba Boni Yayi na Benin

An dai dage zaben ne saboda kasa raba daukacin katinan zabe

Kotun tsarin mulki a jamhuriya Benin ta sanar da dage zaben shugaban kasar zagayen farko na ranar 28 ga watan nan, har zuwa 6 ga watan Maris mai zuwa.

A sanarwa da kotun ta fitar da yammacin jiya ta ce an dage zaben ne saboda kasa raba daukacin katinan masu kada kuri'a.

Dama kafin hakan 'yan takara da dama a kasar sun bukaci da gusa zaben saboda tsaiko da aka samu wajen yin katocin dama fara raraba su.